Nigerian

Tambayoyin da wadanda suka sami cikin-wajen-mahaifa (ectopic pregnancy) da mazajensu suke yawan yi;

1. Irin wannan cikin zai sake faruwa dani kuwa?
To lalle ne muddin wannan irin matsala in ya same ki, to hadarin ya sake faruwa yana karuwa wajenki. Haka din, yakan kai ninki goma daga cikin dari in an kwatanta ki da sauran mata wadanda hadarin abkuwar irin wannan cikin daya zuwa biyu ne kurum daga cikin dari. Amma kuma sai kiyi la’akari da cewa, kina iya yin ciki ba matsala tun daga kashi 50 har zuwa 80 cikin dari bayan kin sami kanki cikin waccan matsalar na cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaiba.

2. To menene alkalummar sa’a ko rashin sa na yin cikin da ba matsala?
To baki daya dai, kina iya samun cikin da ba matsa har zuwa kashi hamsin zuwa tamanin daga cikin dari. In cikin anyi shine da taimakon likita (IVF), sa’an tafi dan kyau, da yake hadarin yin bari da kuma cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa ba ya kan karu bayan irin wannan cikin har zuwa ribi Hudu. Da zaran cikin nan ya habaka, musamman ma har ya wuce wata ukun farko, to sa’ar kai wa har karshe yana kwatankwacin sauran masu ciki. Har ila yau, waccan matsalar bata shafar abin da ya rage na sauran wattanin cikinki da nakuda ko haihuwa ba. Saboda haka ma, ba wani bukatar neman ganin likitan haihuwa don gwaje-gwaje na musamman, muddin dai cikin ya kan kama.

3. Yaushe ne jini na zai dauke?
Ganin jinni, bayan cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa ba sanennen abu ne. Jinin ya na gudana ne bayan zubewar bangon cikin mahaifar. Tsawonsa baya wuce tsawon jinin al’ada, sai dai wani lokacin ya kan iya tsawaita. Sai a nemi shawarar Likita in akwai wani damuwa.

4. Ko yaushe ne kuma zan sake kokarin yin Ciki?
Babu wani takamammen hujja da ya dangana karawur hadarin yin cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa ba, da daukan ciki, cikin gaggawa bayan waccan matsalar. Sai dai, idan am baki taimako da maganin Methotrexate, to yana da kyau ki dakata a kalla wata Uku kafin daukar wani cikin. Domin, shi wannan maganin yana iya lahanta sabon dan tayi a watannin farko na ciki. Saboda haka ake bada shawarar jinkirta yin ciki ta hanyoyin tabattattu na hana daukar ciki.

5. Likitoci sun gaya mini cewar anyi min tiyatar Huji cikin Hannun Mahaifa na ne(salpingostomy), ko menene bayanin sa?
Wannan wani dan yanka ne ake yi akan Bututun Mahaifa, wajen da wannan Cikin ya makale don a cireshi. Sannan sai a barshi ya warke da kansa ba tare da an cire Bututun gaba daya ba. Yana da kyau yin haka musamman ma, in dayan bututun shima na da lahani.

6. A nawa tiyatar, gabaki dayan Bututun-Mahaifa na hagu ne aka cire. Kana ganin sa’ar daukar ciki na zai fi kyau ne in bangaren sa ne kawai aka cire?
Ko dayake hankali zai fi kwanciya ta tsammanin furucin ki, amma, hujjoji sun nuna ba ban-banci wajen daukan ciki bayan kowane dayan biyun.

7. Da yake nawa cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifar ya fashe, sai da aka bude gangan ciki na don tiyatar sa, ba irin tiyatar ramin-makulli ba. To wannan yana iya dakushe min yin ciki nan gaba?
A’a, koda yake, sanannen abu ne cewa tiyatar ramin-makulli yana da fa’idodi da yawa, kamar karanci tabo, makadanci kwanakin kwanciya a asibiti, da saurin warkewa bayan tiyatar. Duk da haka, ba wani hujjar ficewarsa a kan sauran nau’in tiyatu dan gane da daukar ciki.

8. To, ko yaushe jinin al’ada na zai dawo?
To, in da ma al’adar ki bata da matsala kafin yin cikinki, to sai ki tsammaci jininki ya dawo cikin mako Hudu zuwa Shida. In kuwa, da ma al’adarki da matsala, to kina iya ganin canji. In har kika ga jinkiri mai tsawo, to sai ki nemi taimakon likitarki.

9. Mai zai faru in lambar jina na Rhesus-maras ne?
To, in wannan ne cikin ki na farko, kina bukatan alluran maganin-anti D. Wato, a yi alluran cikin kwanaki uku daga yin tiyatar. In kuwa baki san lambar jininki ba, to sai ki bincika ta wajen likitanki. A kan yi gwajin lambar jini lokacin da kika sami irin wannan matsalar ciki.

10. Ko akwai yadda zan kare kaina da abkuwar irin wannan matsalar nan gaba?
A’a, ba wata makafar kare kai daga irin wannan matsala. Ko magani, ko kuma cire Bututun-Mahaifa duk basu taimakawa. Ma fi a’ala dai, shine ki guji daukar wani cikin ta hanyoyin da suka dace kamar magunguna ko amfani da kwaroron roba. In kuwa kina dauke da kwayoyin cuta ne da ke kawo wannan matsalar, to sai ki bukaci ganin likita don baki magani. Sai kiyi hattara da zaran kin yi sabon ciki, domin kina iya kuma samun irin waccan cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa ba. In hakane, to gane shi da wuri, da kuma yin tiyatarsa yana iya taimaka miki sosai.

11. Ko zan iya amfani da wayar-cikin-mahaifa (IUCD)?
E, babu matsala ta yin amfani da wayar-cikin-mahaifa bayan waccan matsalar ta cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa ba. Wayar Tagulla (copper) ko ta Mirena duk basu da hatsari. Babu hujjoji masu kyau da ke danganta waccan matsalar na cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifaba, da amfani da wayar-cikin-mahaifa. Amma, in wayar-cikin-mahaifar nan ta kasa hana daukar ciki, to kina iya kara samun hadarin yi wu war cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa ba.

12. Ko zan iya amfani da kwayar-hana-daukar-ciki (mini pill)?
E, matukar dai kin yi amfani da shi kamar yadda ya dace, to zai iya hana daukar ciki. In har kuwa, baza ki iya tunawa da shan kwayar akai-akai ba, to wannan ba zai zama hanya mafi kyau na hana daukar ciki ba. Ko da yake, wannan kwayar bata kara hadarin yin cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa ba.

13. Ko Jaririn da zan haifa nan gaba zai zo da wani illa?
Faruwar cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa baya kara hadarin haihuwar jariri mai illa. Sai dai, in am miki amfani da maganin Methotrexate bayan kasancewar waccan ciki, to yana da kyau ki kaurace wa daukan ciki har bayan wata Uku. In kuwa, ba a dace ba, har kika dauki ciki, cikin wadannan watanni Uku, to sai ki sanar da likitanki don ya tura ki wajen likitan-musamman wanda zai yi wasu gwaje-gwaje don gane ko wannan Jaririn da kike dauke da shi ya shafu da lahani. Kuma zai baki bayanin yadda za a magance wannan illar.

14. Me yakamata in yi da zaran na dauki ciki?
To yana da muhimmanci ki nemi shawarar Likitanki tun da mako na biyar. Za ayi hoton Ultrasound don a tabbatar da cewa cikin ya zauna cikin-mahaifa. In kuwa a kwai shakkar kasancewar cikin bai zauna da kyau, to lalle ne a ci gaba da gwaje-gwaje har a tabbatar cikin ‘yan makonnin gaba.

15. Zan bukaci Tiyatar-Haihuwa (caeserean section)?
Ba wani hujjar da ya ce dole ne ayi Tiyatar-Haihuwa ga wadda ta sami cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa ba. In ki ka nace sai anyi Tiyatar-haihuwa mi ki, to kuwa hadarin cikin-da-bai-zauna-cikin-mahaifa ba ya kan dan karu. Domin kuwa hadarin da ke tattare da kamuwa da kwayoyin cuta sun fi, bayan Tiyatar-Haihuwa in an kwatan ta da wan da ta haihu da kan ta.